Kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa 'yan sandan sun danganta fashewar wata ma'ajiyar bama-bamai na kungiyar 'yan ta'adda ta "Tehreek-e-Taliban Pakistan", amma wasu mazauna yankin sun tabbatar da cewa harin da sojoji suka kai shi ne ya haddasa shi.
Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: 'Yan sandan Pakistan sun sanar da cewa: Wata fashewa a wani ma'ajiyar harsasai mallakar 'yan ta'adda a arewa maso yammacin kasar ya kashe mutane 24 da suka hada da mata da kananan yara 10. Lamarin ya faru ne a cikin kwarin "Tira" da ke gundumar Khyber a lardin Khyber Pakhtunkhwa.
Your Comment